Wannan umarni na shugaban ya biyo bayan kisan soji 9 da wasu fararen hula da dama aka yi bayan wani kwanton bauna da 'yan Boko Haram din suka yi wa sojin kasar a kokarinsu na kwato masu binciken kasa na kamfanin mai na kasar da wasu malamai na jam'iar Maiduguri da Boko Haram din suka yi garkuwa da su a kwanakin da suka gabata. Tuni dai ma'aikatar tsaron kasar ta bakin ministanta Janar Mansur Dan Ali mai ritaya ta ce ta matsa kaimi a yaki da Boko Haram din musamman ma dai a wannan lokaci da suke zafafa kai hare-hare.
Jami’ar Maiduguri ta tabbatar da kashe wasu ma’aikatanta a harin da ‘yan kungiyar Boko Haram suka kai wa masu binciken man fetur a Magumari da ke cikin jihar Borno a Najeriya.288